in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya shirya liyafar maraba ga mahalarta bikin baje kolin CIIE
2018-11-05 09:22:53 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da uwar gidan sa Peng Liyuan, sun shirya wa mahalarta bikin baje kolin CIIE daga sassan duniya daban daban liyafar maraba.

A Litinin din nan ne dai za a bude taron baje kolin na CIIE irin sa na farko a birnin Shanghai, wanda wani jigo ne na bunkasa kudurin kasar Sin, na kara bude kofar kasar ga kasashen waje a matakin koli, da fadada kasuwarta ta kasa da kasa.

Cikin kwanaki 6 masu zuwa, wakilai daga kasashen duniya da yankuna da kungiyoyi da hukumomin daga sassa daban daban da yawansu ya kai 172, za su baje hajojin su masu kunshe da fasahohin ci gaban su, domin yin musaya da sauran sassa.

Yayin liyafar ta maraba, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, sama da kamfanoni 3,600 daga kasashe daban daban, za su tattauna domin zakulo hanyoyin samar da ci gaba tare da takwarorin su na bangaren masu sayayya daga Sin da na sauran kasashe. Kaza lika mahalarta baje kolin za su tattauna game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayayyar kasa da kasa.

Ya ce wannan baje koli mai matukar alfanu, ana sa ran zai samar da damammaki, na cimma moriya ga abokan kasar Sin mahalartan sa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China