in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta
2018-11-04 19:52:11 cri
A yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana a birnin Shanghai da takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda yake ziyara a kasar Sin.

A yayin ganawarsu, Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata kasashen Sin da Kenya su yi amfani da sakamakon da aka samu a yayin taron kolin FOCAC da aka yi a watan Satumba a Beijing da damar bunkasa "ziri daya da hanya", su yi kokarin kara ciyar da huldar hadin gwiwa irin ta abota da aka kafa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu gaba. Shugaba Xi ya kara da cewa yana maraba da shugaba Kenyatta da ya halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko, kuma bangaren Sin zai taimakawa bangaren Kenya wajen kara darajar kayayyakinsa da gogayyarsu a kasuwa, kuma zai kara shigowa da kayayyaki daga kasar Kenya.

A nasa bangaren, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, yana farin cikin zuwa kasar Sin domin halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar karo na farko, yana sa ran amfani da wannan dama domin karfafa huldar dake tsakanin kasashen Kenya da Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Sannan ya godewa kasar Sin, bisa daukar muhimmin matakin kara bude kasuwarta ga kasashen waje, har ma ta mayar da Afirka wani muhimmin bangare cikin manufarta ta bude kofarta ga waje. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China