in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin CIIE a birnin Shanghai
2018-11-05 11:41:41 cri

Yau Litinin, aka bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko wato CIIE a birnin Shanghai na kasar, shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bude bikin, inda kuma ya gabatar da wani muhimmin jawabi.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, shirya bikin CIIE wata babbar manufa ce da kasar Sin ta fitar, wajen bude kofa ga waje, kuma wani muhimmin mataki ne da Sin ke dauka, wajen bude kasuwarta ga duniya. Lamarin da ya shaida matsayin kasar Sin, na goyon bayan tsarin yin cinikayyar kasa da kasa, da sa kaimi ga yin ciniki maras shinge.

Domin kara bude kofar kasar Sin ga ketare, Shugaba Xi ya sanar da cewa, a shekaru 15 masu zuwa, kasarsa za ta shigo da kayayyaki, da ayyukan hidima masu darajar dalar Amurka biliyan 30000 da biliyan 10000, kaza lika Sin za ta inganta bude kofa ga kasashen ketare ta fuskoki guda biyar, ciki har da inganta karfin shigo da kaya, da sassauta izinin zuba jari a Sin, da kafa muhallin cinikayya mai kyau kwarai a duniya, da habaka sabbin fannonin da za a bude kofa a kai, da kuma inganta hadin kai na bangarori da dama, da tsakanin bangarori biyu da dai sauransu.

Game da tattalin arzikin kasar Sin, Xi Jinping ya furta cewa, idan an kwatanta da sauran manyan kasashe a fannin tattalin arziki, kasar Sin tana sahun gaba a duniya ta fuskar karuwar tattalin arziki. Ya ce Sin tana da kyawawan yanayin kiyaye bunkasuwar tattalin arzikinta cikin dogon lokaci ba tare da tangarda ba. A ganinsa, tattalin arzikin kasar Sin tamkar wani teku ne maimakon tabki. Ko da guguwar iska ba za ta kawo illa ga teku ba. Ya ce tabbas tattalin arzikin Sin zai kama hanyar neman samun bunkasuwa mai inganci yadda ya kamata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China