Xi ya ce, yanzu ana kokarin kyautata tattalin arzikin duniya, a sa'i guda ana samun farfadowar ra'ayin bada kariya da ra'ayin gefe guda, tare kuma da fuskantar kalubale wajen neman dunkulewar tattalin arzikin duniya, ban da haka ana gamuwa da matsaloli a fannonin ra'ayin bangarori da dama, da tsarin cinikayya cikin 'yanci, har zuwa yanzu ana fuskantar rashin tabbaci. Don haka, kamata ya yi a kara fahimtar yanayin da ake ciki, da tsayawa kan aniyar bude kofa da hadin kai, don tinkarar hadari da kalubaloli tare. (Bilkisu)