Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya furta yau a birnin Shanghai, cewar idan an kwatanta da sauran manyan kasashe a fannin tattalin arziki, kasar Sin tana sahun gaba a duniya ta fuskar karuwar tattalin arziki. Ya ce Sin tana da kyawawan yanayin kiyaye bunkasuwar tattalin arzikinta cikin dogon lokaci ba tare da tangarda ba.
A ganinsa, tattalin arzikin kasar Sin tamkar wani teku ne maimakon tabki. Ko da guguwar iska ba za ta kawo illa ga teku ba. Ya ce tabbas tattalin arzikin Sin zai kama hanyar neman samun bunkasuwa mai inganci yadda ya kamata. (Kande Gao)