in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#CIIE# Sin za ta kaddamar da manyan manufofi guda uku don inganta bude kofa ga ketare a wasu yankunan kasar
2018-11-05 11:08:51 cri
Yau Litinin aka sanar da cewa, za a kaddamar da manyan manufofi guda uku don inganta bude kofa ga ketare a wasu yankuna, ciki har da Shanghai.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a birnin Shanghai, cewa kasarsa za ta kafa sabbin yankuna a yankin gwajin cinikayya cikin 'yanci na Shanghai, don nuna goyon baya ga birnin wajen samar da fasahohi mafi yawa ga duk fadin kasar, a fannonin inganta zuba jari, da samar da sauki ga cinikayya cikin 'yanci, kana kuma za a kafa sashen yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, a kasuwar cinikin takardun hada-hadar kudi ta Shanghai, da kuma yin gwajin tsarin yin rajista, don nona goyon baya ga birnin, wajen raya cibiyar kudi ta duniya, da ta yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta duniya. Baya ga haka, za a nuna goyon baya ga dunkulewar yankin delta na kogin Yangtse, ciki har da Shanghai, da lardunan Zhejiang da Jiangsu da dai sauransu, kuma za a mayar da aikin a matsayin daya daga cikin manysan tsare-tsaren kasar, wanda zai hade shawarar"Ziri daya da hanya daya", da shirin samun ci gaba cikin hadin gwiwa tsakanin Beijing, Tianjin da Hebei, da shirin ci gaban zirin tattalin arziki na Yantse, da na raya babban yankin bakin teku na Guangdong, da Hong Kong da Macau, ta yadda za a kayutata aikin bude kofa ga kasashen ketare, da yin kwaskwarima a cikin gida a fannin yankunan. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China