Gwamnan lardin Bay, Ali Wardhere Doyow, ya fadawa manema labarai cewa al'ummar yankin suna bayar da gudumowar jini domin ceto rayukan wadanda suka jikkata a harin tagwayen boma boman na garin Baidoa, ya kara da cewa, wadanda suka samu munanan raunuka za'a garzaya da su zuwa birnin Mogadishu a yau Lahadi domin yin musu magani. (Ahmad Fagam)