in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji sun kashe mayakan al-Shabab 8 a kudancin Somalia
2018-10-16 10:54:51 cri
A jiya Litinin sojojin Somaliya sun kashe kimanin mayakan al-Shabab 8 da kuma jikkata wasu da dama a wani musayar wuta da suka yi a wani yanki dake kudancin kasar.

Ismail Khalif Shire, kwamandan runduna ta 60 ta sojojin Somalia, ya fadawa manema labarai cewa soja guda ya rasa ransa, wasu sojojin kuma sun samu raunuka a lokacin da suka yi arangama da mayakan a yankin Daynunay mai tazarar kilomita 30 daga garin Baidoa.

Shire ya ce, "mun kashe mayakan al-Shabab 8 da jikkata wasu da dama, mun tarwatsa mayakan, mun kwace yankin, sannan mun kwaso gawawwakin su zuwa wannan wajen".

Sai dai mayakan al-Shabab sun yi ikararin kwace ikon yankin Daynunay tare kwato makamai daga sansanin sojojin.

Fadan na baya bayan nan ya zo ne kwanaki 2 bayan da mayakan al-Shabab suka kaddamar da harin kunar bakin wake a ranar Asabar lamarin da yayi sanadiyyar rayukan mutane 22 da raunata wasu 36 a garin Baidoa dake shiyyar Bay. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China