Ugas Hassan Abdi, ministan yada labarai na jahar kudu maso yammacin kasar ya ce, a kalla mutane 10 ne suka mutu, kana wasu sama da 20 kuma suka jikkata a harin. Mafi yawan wadanda suka mutu fararen hula ne, in ji ministan.
Wadanda suka mutu, galibinsu matasa ne, da suka taru domin shan shayi a lokacin da dan kunar bakin waken ya kaddamar da harin inda ya hallaka kansa nan take a wani gidan sayar da abinci kana mintoci kadan bayan harin farko, aka sake kaddamar da wani harin a otel din Bilan dake tsakiyar garin.
Abdifitah Muhidin, wanda ya ganewa idonsa faruwar lamarin, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya ga gawawwakin mutane da dama kwance a kasa bayan kaddamar da harin.
Kungiyar mayakan al-Shabab ta dauki alhakin kai harin, ta ce mayakanta ne suka kashe sama da mutane 20. (Ahmad Fagam)