Kungiyoyin sun hada da na sarrafa kayan amfanin gona, da na hada takalman fata, da kere kere, da sinadaran albarkatun man fetur, da kayayyakin jiragen kasa, da kayayyakin tsaro, da fasahar sadarwa ta zamani da dai sauransu, inda za su halarci tarurruka daban daban domin tallata kayayyakin da kasar ke samarwa da kuma neman hanyoyin zuba jari.
"Babban abin da za'a mayar da hankali shi ne yadda za'a ja hankalin masu sha'awar zuba jari da masu sayen kayayyakin da kasar Afrika ta kudu ta sarrafa," in ji kakakin hukumar DTI Sidwell Medupe.
Ministan ciniki da masana'antun kasar Afrika ta kudu Rob Davies, shi ne zai jagoranci tawagar wakilan kasar wanda zai gabatar da jawabi a taron dandalin zuba jari na kasar Afrika ta kudu a yayin bikin baje kolin na CIIE. (Ahmad Fagam)