in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani: Baje kolin kayan da ake shigo da su kasar Sin zai samar da daidaiton ciniki tsakanin Sin da Afrika
2018-11-04 15:38:51 cri
Wani masanin harkokin cinikayya na kasar Ghana ya ce baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na Shanghai karo na farko wato CIIE a takaice wata babbar dama ce da ya kamata kasashen Afrika su yi amfani da ita wajen karfafa samun daidaito a harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

Edward Kareweh, sakatare janar na kungiyar 'yan kasuwa manoma ta kasar Ghana ya ce daya daga cikin muhimmiyar damar da baje kolin zai samarwa kasashen Afrika shi ne yadda za su bunkasa fannin masana'antunsu ta yadda hakan zai kara kyautata alakar cinikayya dake tsakanin Sin da nahiyar Afrika, ya bayyana hakan ne a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya.

Kareweh ya ce, za'a iya cimma wannan buri ne idan har kasashen Afrika suka yi kyakkyawan amfani da wannan damar wajen kyautata tsara manufofin da suka shafi cigaban masana'antun nahiyar da kayayyakin da suke samarwa ta yadda za su iya yin gogayya da sauran kayayyaki a kasuwannin kasar Sin.

Kwararren ya buga misali da cewa, idan har kasashen Afrika suka koyi darasi ta hanyar halartar bikin baje kolin za su fahimci yadda za su kirkiro wasu tsare tsare da za su janyo hankalin Sinawa masu zuba jari a Afrika domin samar da kayayyakin da za su yi gogayya a kasuwanni.

Ya ce maimakon yadda kasashen Turai suke kwasar kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa daga Afrika zuwa kasashensu, daga bisani kuma su sarrafa su sannan su sake dawo da su a sayarwa mutanen Afrika, masanin tattalin arzikin ya ce hakika Sin ta fi ba da damammakin yin hadin gwiwa da nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China