in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwar kasar Ghana na sa ran baje kolin CIIE zai inganata harkokin cinikayya tsakaninsu da kasar Sin
2018-11-02 10:33:59 cri
'Yan kasuwar kasar Ghana masu fitar da kayayyaki, na ganin taron baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin na farko wato CIIE da za a yi a makon gobe, kyakkyawar dama ce ta karfafa dangantakar cinikayya da kasar Sin.

Shugaban hukumar daidaita farashin Cocoa ta Ghana, Joseph Boahen Aidoo, ya bayyana fatan taron zai bude sabon babi ga harkar fitar da Cocoa ga kasar dake yammacin Afrika.

Bayan Cote d'Ivoire, Ghana ita ce ta biyu wajen fitar da Cocoa a duniya. Gwamnati da masu tsare-tsare sun yanke shawarar Cocoa ne zai jagoranci kayayyakin rumfar Ghana a wajen baje kolin.

Joseph Aidoo, ya ce ya yi ammana cewa, za su iya fadada kasuwar su a kasar Sin. ya ce la'kari da yawan jama'a da ya kai miliyan 1.3, ko da kaso 1 na kasuwar su ka samu, abu ne mai yawa.

Shi kuwa shugaban sashen fitar da kayayyaki na ma'aikatar cinikayya da masana'antu ta kasar Ebo Quaison, cewa ya yi, Ghana na daya daga cikin kasashen da aka gayyata don su kafa rumfa a wajen taron, inda ya ce za su baje Cocoa da kayayyaki masu nasaba da shi, duk da cewa za su je taron baje kolin da kayayyaki daban- daban sama da 50.

Ya ce ba kamar sauran tarukan baje koli da 'yan kasa da baki ke takarar wurin kafa rumfa da damarmaki tare ba, wannan ya banbanta, domin baje koli ne na kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China