Sai dai duk da saurin karuwar harkokin cinikayya tsakanin Sin da Kenya, kasashen biyu na fuskantar matsalar rashin daidaiton ciniki. Game da wannan, Kikwai ya ce, taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka gudanar a birnin Beijing ya nuna cewa, kasar Sin za ta habaka shigo da kayayyaki daga kasashen Afirka, don haka, kara shigo da kayayyaki daga kasashen Afirka zai zama sabon bangaren da sassan biyu za su mai da hankali a kai a hadin gwiwarsu. Ya ce, "a sabo da haka ne, wasu kamfanonin kasar Kenya za su halarci bikin, kuma a lokacin da suke ciniki, bankin kasuwancin kasar Kenya zai iya kasancewa kyakkyawan abokin hadin gwiwa a gare su." (Lubabatu)