Wannan shi ne ra'ayin galibin 'yan kasuwa da kamfanoni da masu sharhi kan al'amuran ci gaba na Afrika ta kudu da suka gana da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Wani mai sharhi kan harkokin ci gaba a kasar Afrika ta kudu Ruben Richards, ya ce bikin zai bada damar jure yanayin rashin tabbas da tattalin arziki ke ciki.
Ruben Richards wanda shi ne shugaban gidauniyar Ruben Richards, kuma tsohon sakataren zartarwa na hukumar warware sabani ta Afrika ta kudu, ya ce wannan dama ce ta musamman da za a gwada kayayyakin kasarsa a babbar kasuwa da kuma yanayin tattalin arziki mai sarkakiya.
Ita kuwa shugabar cibiyar kasuwanci da masana'antu ta Cape, Janine Myburgh, shawartar 'yan kasuwa masu fitar da kayayyaki ta yi, da su rika shiga bukukuwa irin wannan, domin yana bada kyawawan damarmakin haduwa da masu sayayya da kuma gano damarmaki ko gibi a kasuwa. (Fa'iza Mustapha)