in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Standard Bank: Ya kamata Afrika ta yi amfani da damar baje kolin CIIE
2018-11-05 09:30:35 cri
A yayin da a yau Litinin aka shirya kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa wato CIIE a takaice a birnin Shanghai na kasar, wani kwararre a bankin Standard Bank ya ce, kamata ya yi kasashen Afrika su yi amfani da wannan muhimmiyar dama domin cimma nasarar bunkasa harkokin cinikayyarsu a kasuwannin duniya.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, shugaban sashen kasuwanci na bankin Standard Bank, Vinod Madhavan, ya ce bude kofar shigar da kayayyakin da kasar Sin ke ci gaba da yi zuwa kasarta ya kasance wata muhimmiyar dama ce da Afrika ta samu a daidai lokacin da ya dace.

Ya ce baje kolin na CIIE zai kara bunkasa hadin gwiwar ciniki da tattalin arzikin kasa da kasa, kuma zai daga matsayin harkokin cinikayyar kasa da kasa, kana zai kara kyautata ci gaban tsarin bude kofa ga tattalin arzikin duniya.

Madhavan ya kara da cewa, CIIE zai kara bayyana muhimmancin gamayyar hadin gwiwar kasa da kasa. Zai bunkasa ci gaban Afrika kuma zai tabbatar da kyautatuwar tattalin arzikin kasashen wanda ya ta'allaka kan tsarin bude kofa, da yin mu'amala tare, da bin tsarin dokoki na kasa da kasa, domin samun ci gaba da cin moriya daga baje kolin shigar da kayayyakin.

Ya ce manufar kasar Sin na shigo da karin kayayyaki daga kasashen ketare, da kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa, da ayyukan hidima sun yi matukar dacewa da burin da kasashen Afrika suke da shi a halin yanzu na neman bunkasuwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China