in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar 'yan sanda ta nahiyar Afrika ta dora damarar yaki da ta'addanci da laifuka tsakanin iyakoki da na kafar intanet
2018-10-17 10:23:14 cri

Hukumar 'yan sandan nahiyar Afrika, ta yanke shawarar kafa wasu rukunoni 3 da su jajirce wajen yaki da ayyukan da ake aikatawa tsakanin iyakokin kasashe da na kafar intanet da kuma yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Shugaban kwamitin sulhu na Tarayyar Afrika Smail Chergui ne a bayyana haka, yayin da ake kammala zaman babban zauren hukumar karo na 2, wanda ya gudana ranakun Litinin da Talata a birnin Algiers.

Ya ce kasashe mambobin hukumar, sun amince su kafa kwamitocin hadin gwiwa 3 domin yaki da wadancan manyan laifuka 3.

Ya kara da cewa, mambobin sun kuma amince da gudanar da taro a ko wace shekara, domin tsara manufofi da matakai iri guda na nahiyar da za su gabatar yayin taron hukumar 'yan sanda ta duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China