Yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jaridu, Mangaliso Ndlovu ya ce, kamfanonin Zimbabwe ba su shiga cikin kasuwannin kasar Sin sosai ba. A wajen taron koli na Beijing, na dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya baiwa kamfanonin Afirka kwarin-gwiwar shiga cikin kasuwannin kasar Sin, al'amarin da ministan ya ce ya karfafa musu gwiwa sosai. Mangaliso Ndlovu, ya kara da cewa yana fatan yin amfani da wannan dama wajen kara fahimtar hajjojin da masu sayayyar kasar Sin suke sha'awa da ma'aunin hajjojin kasar, ta yadda za su kara shiga cikin kasuwannin kasar ta Sin.(Murtala Zhang)