Yau a nan birnin Beijing shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi ganawa da firayin ministan kasar Pakistan Imran Ahmed Khan Niazi wanda ke yin ziyara a kasar Sin.
Xi ya yi maraba da zuwan Mr. Khan Sin, yana mai bayyana cewa, kasashen Sin da Pakistan aminai ne a ko da yaushe, duk da cewa yanayin da kasashen duniya ke ciki ya samu manyan sauye-sauye, amma huldar dake tsakanin kasashen biyu, ta samu ci gaba yadda ya kamata, kuma tana cike da kuzari. Kaza lika al'ummun kasashen biyu sun samu moriya daga hadin gwiwar dake tsakaninsu, wanda hakan ke sa kaimi ga ci gaban kasashen duniya baki daya.
Xi ya yi nuni da cewa, nan gaba kamata ya yi sassan biyu su kara zurfafa cudanyar dake tsakaninsu, ta yadda za su gudanar da hadin gwiwa a dukkanin fannoni.
A nasa bangare, Imran Khan ya bayyana cewa, kasarsa tana jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu, tana kuma fatan za ta iya koyi daga fasahohin da kasar Sin ta samu, a fannin raya kasa, da yaki da talauci, da dakile cin hanci da rashawa. Ya ce Pakistan tana son kara zurfafa huldar dake tsakaninta da kasar Sin, domin kara ciyar da tattalin arzikin Pakistan gaba yadda ya kamata.(Jamila)