in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya aike da sakon taya murna ga taro game da gyare gyare da bude kofa da yaki da fatara
2018-11-01 20:27:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron kasa da kasa, game da gyare gyare, da bude kofa, da yaki da fatara na kasar Sin, wanda aka bude a nan birnin Beijing.

Shugaba Xi Jinping, wanda ya aike da sakon na sa ta cikin wata wasika a Alhamis din nan, ya ce a matsayin kasar Sin na kasa mai tasowa, wadda ke da al'umma mafi yawa a duniya, ta dade tana taka muhimmiyar rawa, wajen bunkasa yaki da fatara a daukacin sassan duniya.

Ya ce, sama da shekaru 70, tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, JKS ta jagoranci al'ummar Sinawa wajen gudanar da aiki tukuru, da dogaro da kai, da gwagwarmaya ta yaki da talauci. Ya ce musamman cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ta bude wani sabon shafi na aiwatar da sauye sauye a cikin gida, tare da bude kofa ga kasashen waje, a lokaci guda kuma, ta fara aiwatar da gagarumin aikin dakile fatara da talauci, irin sa mafi shahara a tarihin rayuwar bil Adama.

Shugaba Xi ya kara da cewa, cikin shekaru 40 da suka gabata, al'ummar Sinawa sun yi namijin kokari, wajen fitar da al'ummar kasar sama da miliyan 700 daga kangin talauci, tare da samar da wani yanayi mai ban makaki a tarihi, na ciyar da rayuwar bil Adama gaba.

Xi ya kuma bayyana aniyar kasar sa, na ci gaba da aiki da dukkanin sassa, wajen fadada yakin da duniya take yi da fatara, tare da cimma kudurin rage talauci, karkashin manufar MDD ta wanzar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030.

Daga nan sai ya yi fatan mahalarta taron za su yi musayar bayanai, da kwarewa, game da batutuwan da suka jibanci rage fatara, su kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin. Kana su yi musayar gogewa, ta yadda za a kai ga gina al'umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China