in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya zanta da Trump
2018-11-02 10:35:05 cri
Shugaban kasar Sin ya zanta da takwaransa na Amurka Donald Trump ta wayar tarho a jiya Alhamis.

Donald Trump ya ce, kara yin mu'amala tsakanin shugabannin Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, kuma yana fatan ganawa da shugaba Xi yayin taron kolin G20 da za'a yi a kasar Argentina, inda za su samu damar zurfafa shawarwari kan wasu muhimman batutuwa. Trump ya ce kasarsa na maida hankali sosai kan hadin-gwiwarta da kasar Sin ta fannin tattalin arziki da cinikayya, kuma tana fatan ci gaba da fadada fitar da hajjojinta zuwa kasar Sin. Ya kuma kara da cewa, yana goyon-bayan kamfanonin Amurka su je birnin Shanghai don halartar bikin baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko wato CIIE a takaice a mako mai zuwa.

A nasa bangaren, shugaba Xi Jinping ya bayyana niyyarsa ta yin shawarwari da Trump yayin taron kolin G20 a kasar Argentina. Xi ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, an samu sabani a tsakanin Sin da Amurka ta fannin ciniki da tattalin arziki, al'amarin da ya haifar da illa ga wasu sana'o'in kasashen biyu gami da cinikayya a fadin duniya. A makon gobe ne, za'a fara bikin baje-kolin CIIE a birnin Shanghai na kasar Sin, abun da ya bayyana kyakkyawar niyyar gwamnatin kasar Sin ta kara shigo da kayayyakin kasa da kasa da fadada bude kofarta ga kasashen ketare. Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata kungiyoyin tattalin arzikin kasashen biyu su kara yin mu'amala da cudanya tsakanin juna, don lalibo bakin zaren daidaita matsalar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China