in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya aike da sakon taya murna ga kungiyar kawancen kasashen Ziri Daya da Hanya Daya a fannin Kimiyya
2018-11-04 16:17:26 cri
A yau Lahadi ne Shugaba Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga bikin kaddamar da kungiyar kawancen kasashen Ziri da Hanya Daya, a fannin kimiyya.

Cikin wasikar, shugaba Xi Jinping ya ce inganta hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha tsakanin kasashe, muhimmin bangare ne ga ginin shawarar ziri daya da hanya daya, kana zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar jama'a da samar da ci gaba da kuma tunkarar kalubale na bai daya.

Ya kuma bayyana fatan masana kimiyya daga kasashe daban-daban za su yi amfani da kawancen a matsayin dandalin aiwatar da hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha da karawa masu basira karfin gwiwar kirkire-kirkire da kasuwanci a fannonin.

Shugaba Xi ya kuma yi kira ga masana kimiyya, su bada gudunmuwarsu ga inganta sadarwa tsakanin mutane da tabbatar da dorewar ci gaban zaman takewa da tattalin arziki da kirkiro tafarkin kirkire kirkire mai kare muhalli da kuma gina al'umma mai kyakkyawar makoma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China