in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya jaddada aniyar aiwatar da tsarin gurguzu mai halayyar musamman na Sin a fannin karfafar mata
2018-11-02 19:10:34 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar aiwatar da tsarin gurguzu mai halayyar musamman na Sin, a fannin karfafar mata, da yi musu kaimi wajen cimma dukkanin nasarori.

Shugaban na Sin, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne, yayin ganawar sa da wakilan gamayyar kungiyoyin mata na Sin.

Ya ce jagorancin JKS na aiki tukuru wajen tabbatar da ci gaban mata, kuma burin kasar Sin na kara farfado da kasa, shi ne jigon da ya dace da fafutukar ci gaban matan kasar.

Daga nan sai ya yi fatan za a kara maida hankali, wajen bunkasa ayyuka masu nasaba da samar da daidaiton jinsi, da baiwa mata damar taka rawar da ta dace a dukkanin sassa, da zaburar da su wajen shiga a dama da su a bangaren aiwatar da sauye sauye, da samar da ci gaba da daidaito a sassan ci gaban kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China