Da take jawabi ga manema labarai a karon farko, a ofishin majalisar dake Geneva, Maria Espinosa ta ce shugabancinta na gudana ne bisa kudurin kare huldar kasa da kasa.
Ta ce ta yi ammana cewa, hanya daya tilo ne magancewa da warware kalubalen da duniya ke fuskanta ita ce huldar kasa da kasa, tana mai cewa ko da muradun kasa da dangantakar kasa da kasa ba su dace da juna ba, za a iya kare maradun kasa da 'yancin cin gashin kai a lokacin da kasashe ke daukar matakai iri guda kan muhimman batutuwa.
Maria Espinosa ta je Geneva ne don halartar taron harkokin zuba jari na duniya na bana, wanda aka bude jiya Litinin zuwa ranar Juma'a 26 ga wata.
Shugabar babban zauren na MDD, ta kuma shaidawa manema labarai cewa, akwai bukatar bangarori masu zaman kansu, su shiga a dama da su wajen cimma muradun ci gaba masu dorewa. (Fa'iza Mustapha)