Yayin da yake bayani game da jawabin Sakatare Janar din a jiya, mataimakin kakakin majalisar Farhan Haq, ya tunatar cewa, cikin jawabi da ya yi a jami'ar Geneva a watan Mayun da ya gabata, Antonio Guterres, ya yi kira ga gwamnatin Rasha da ta Amurka, su warware sabanin dake tsakaninsu dangane da yarjejeniyar.
A karshen makon da ya gabata ne, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, zai janye daga yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 1987 tsakanin shugaban kasar Amurka na wancan lokaci Ronald Reagan da Jagoran Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev, wadda ta haramtawa kasashen biyu mallaka da kerawa da kuma gwajin makami mai linzami mai cin kilomita 500-5,500.
Bayan sanarwar da shugaba Trump ya yi ne mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya bayyana irin wannan yunkuri a matsayin mai hadarin gaske.
Kamfanin dillancin labarai na kasar TASS, ya kuma ruwaito shi yana gargadin cewa, matakin zai iya janyo kakkausar suka daga al'ummomin duniya da suka jajirce wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya. (Fa'iza Msutapha)