in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta janye harajin shigo da wasu kayayyaki a wurin baje kolin CIIE
2018-11-02 11:26:53 cri
Kasar Sin ta sanar a jiya cewa, za ta janye haraji kan wasu kayayyakin da da za a shigar da su wajen baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar karo na farko wato CIIE.

Ma'aikatar kudi ta kasar Sin, ta sanar a shafinta na intanet cewa, yayin baje kolin da zai gudana daga ranar 5 zuwa 10 ga watan nan, masu sayayya za su samu ragin kaso 30 daga harajin cinikayya da na sayen kayayyaki.

Ma'aikatar ta wallafawa baki masu baje kolin jerin kayayyakin da za su ci wannan gajiya a shafinta na intanet. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China