Kamfanonin Sin da ketare sama da 2800 za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su Sin karo na farko

Ya zuwa yanzu, kamfanoni sama da 2800 wadanda suka zo daga kasashe da yankunan duniya fiye da 130 ne suka yi rajistar halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su Sin na bana ko kuma CIIE a takaice. Kakakin ma'aikatar kasuwanci na kasar Sin Gao Geng, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin za ta kara ba da hidima ga kamfanonin kasashen ketare domin shigo da karin jari kasar.
Za a gudanar da bikin CIIE daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba mai zuwa a birnin Shanghai. Babban taken bikin na bana shi ne "Sabon zamani, makoma ta bai daya". (Maryam)