Fu ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping shi kansa ya bada shawara tare kuma da sanarwa duniya cewa, kasar Sin zata shirya babban taron baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa dasu kasar Sin karo na farko daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwambar bana a birnin Shanghai. Xi Jinping zai halarci bikin kaddamar da taron gami da halartar sauran wasu muhimman ayyuka, haka kuma, akwai manyan shugabanni da jami'an gwamnati da mutane daga bangarori daban-daban na kasashe da yankuna kimanin 150 wadanda za su halarci taron.(Murtala Zhang)