in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe 18 za su halarci baje kolin birnin Shanghai
2018-10-29 19:08:19 cri

Bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugabannin kasashe 18 za su halarci bikin baje kolin kayan da ake shigowa da su kasar Sin, irin sa na farko a tarihi wato CIIE a takaice.

A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, za a gudanar da baje kolin ne a birnin Shanghai, tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba dake tafe.

Da yake zayyana jagororin kasashen da ake sa ran za su halarci wannan baje koli, Mr. Lu Kang ya ce sun hada da Milos Zeman na kasar Czech, da na Cuba Miguel Diaz-Canel, da na janhuriyar Dominica Danilo Medina, da shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, da shugabar Lithuania Dalia Grybauskaite.

Sauran sun hada da shugaban Panama Juan Carlos Varela, da na El Salvador Salvador Sanchez Ceren, da na Switzerland Alain Berset. Sai kuma firaministan tsibirin Cook Henry Puna, da firaministan Croatia Andrej Plenkovic, da na Masar Mostafa Madbouly, da na Hungary Viktor Orban.

Har ila yau akwai firaministan Georgia Mamuka Bakhtadze, da na Lao Thongloun Sisoulith, da na Malta Joseph Muscat. Sai kuma firaministan Pakistan Imran Khan, da na Rasha Dmitry Medvedev da kuma na Vietnam Nguyen Xuan Phuc.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China