in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shanghai ta tsara hanyoyin saukakawa mahalarta bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin
2018-10-11 11:11:29 cri
Za'a kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa karo na farko, a ranar biyar ga watan Nuwambar bana a birnin Shanghai, inda gwamnatin wurin ta tsara wasu hanyoyi na saukakawa mahalarta bikin, ciki har da shirya wasu hanyoyin yin yawon bude ido 45, gami da ayyukan bunkasa zuba jari 30, wadanda suka shafi bangarorin yin kere-kere bisa fasahohin zamani, da cinikayya, da hada-hadar kudi, da al'adu da kiwon lafiya da makamantansu.

Makasudin shirya wadannan ayyuka shi ne, tallata birnin Shanghai ta fuskar kasuwanci, da inganta mu'amala da harkokin zuba jari tsakanin yankuna daban-daban na Shanghai ga tawagogi masu halartar bikin baje-kolin. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China