Game da haka, Robert Kuhn, wani masanin ilmin harkokin kasar Sin na kasar Amurka ya nuna cewa, bikin ya nunawa duniya wata alama ta habaka shigo da kayayyaki da Sin ke yi. A cewarsa, wannan bikin baje kolin na CIIE da kasar Sin zata shirya, wani mataki ne na kirkire-kirkire da kasar ta dauka, wanda ya nuna niyyar kasar ta sa himma wajen habaka shigo da kayayyaki. Kasar Sin zata bude kasuwa ga duk duniya, don shigo da kayayyaki daga kasashen daban daban, wadanda zasu biya bukatun jama'ar kasar wajen daga matsayinsu na zaman rayuwa. Ana iya cewa, bikin baje kolin zai samar da dama mai kyau ga kamfanoni da dama na duniya wajen fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Sin.
Baya ga haka, Kuhn ya ce, ta hanyar shirya bikin baje kolin na CIIE, ba kawai kasar Sin ta nuna niyyarta ta bude kasuwa ga duniya ba ne, har ma tana kokarin inganta daidaituwar cinikayya a tsakanin kasa da kasa ta hakikanin matakinta. (Bilkisu)