in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta shafi sama da mutane dubu 350 a arewa maso gabashin Najeriya
2018-10-23 09:40:53 cri
Mahukunta sun sanar da cewa kimanin mutane dubu 357 ne ibtila'in ambaliyar ruwa ta baya bayan nan ta shafa a jahar Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Kimanin gidaje 7,893 da matsalar ta shafa, in ji Muhammad Sulaiman, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa wanda ya bayyana hakan ga 'yan jaridu a Yola, babban birnin jihar.

Ya ce jihar ta aike da kididdigar yawan gidajen da ambaliyar ruwan ta lalata ga hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA dake Abuja, babban birnin kasar, domin neman taimakonta.

Sulaiman ya yi kira ga gwamnatin tarayyar da ta dauki matakan gaggawa wajen tallafawa iyalan da ibtila'in ya shafa.

A kalla mutane 200 ne suka mutu a sanadiyyar ambaliyar ruwa a sassan Najeriya cikin wannan shekarar, wata kididdiga da gwamnatin ta fitar ta nuna cewa, kimanin mutane 1,300 ne aka bada rahoton sun samu raunuka kana wasu mutanen kusan miliyan biyu ambaliyar ruwan ta shafa a yankunan dake kusa da kogin Nija da Benue a Najeriyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China