A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin tana kokarin bunkasa tattalin arziki mai inganci. Sakamakon haka, kasuwarta na da kyakkyawar makoma. Kasar Sin na maraba da dukkan kamfanoni da masana'antun kasashen duniya, da su yi amfani da wannan dama su kara yin hadin gwiwa domin samun sakamakon a zo a gani.
Li Keqiang ya kuma nuna cewa, halin da ake ciki a duniya yana da sarkakiya, ana kuma kokarin aiwatar da manufofin kafa shinge ga cinikayya. Ya ce kasar Sin tana son hada kai da bangaren Holland wajen kare tsarin daidaita batutuwa tsakanin bangarori daban daban, tare da kare tsarin cinikayya cikin 'yanci bisa ka'ida. (Sanusi Chen)