in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministocin kasashen Sin da Belgium sun gana da manema labarai
2018-10-18 10:56:19 cri

A safiyar ranar 17 ga wata bisa agogon wurin, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na kasar Belgium Charles Michel sun gana da manema labarai a fadar Egmont, inda suka amince da cewa, shawarwarin dake tsakaninsu ya samu sakamako na a zo a gani kuma ba tare da boye kome ba.

Firaminista Li ya jaddada cewa, bangarorin biyu za su ci gaba da himmatuwa wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Turai yadda ya kamata, da inganta cudanyar nahiyoyin Asiya da Turai, da ma gaggauta shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Sin da Turai wato BIT. Haka kuma Sin da Belgium suna son kara tuntubar juna a karkashin tsarin MDD da sauran tsare-tsaren da suka shafi bangarori da dama, a kokarin kiyaye manufar kasancewar bangarori da dama da ka'idojin kasa da kasa bisa sanin ya kamata, da ma kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci da tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga sauran kasashe, ta yadda za su ba da gudummawa ga zaman lafiya da kwanciyar hanali da ma ci gaban duniya.

A nasa bangaren, Mr. Michel ya furta cewa, bangarorin Belgium da Sin sun cimma daidaito kan yadda za a kiyaye manufar kasancewar bangarori da dama da tafiyar da harkokin duniya bisa ka'idoji yadda ya kamata. Za su hada kai sosai wajen kiyaye zaman lafiya da na karko da ma ci gaban duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China