Cikin sakonsa, shugaba Xi na kasar Sin ya ce hadin gwiwar da ake yi a fannin zirga-zirgar kumbuna, wani muhimmin bangare ne na abotar dake tsakanin Sin da Faransa, wadda ta shafi dukkan fannoni.
A nasa bangare, shugaba Macron na kasar Faransa, ya ce nasarar da aka samu a wannan karo, ta shaida ci gaban da aka samu a hadin gwiwar da ake yi tsakanin Faransa da Sin, musamman ma a fannin zirga-zirgar kumbuna. (Bello Wang)