in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya aike da sakon ta'aziyya game da hadarin jirgin saman kasar Indonesia
2018-10-30 19:39:18 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta'aziyya, game da hadarin jirgin saman kasar Indonesia ga shugaba Joko Widodo na kasar.

Shugaba Xi wanda ya aike da sakon a Talatar nan, ya bayyana kaduwa, game da rasuwar mutane 189, dake cikin jirgin saman kamfanin Lion na Indonesia.

Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce hadarin jirgin saman ya tayar da hankalin sa. Ya ce a madadin shi kan sa, da gwamnatin Sin da jama'ar ta, yana mika sakon ta'aziyya ga wadanda hadarin ya rutsa da rayukan su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China