in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Japan
2018-10-26 20:35:31 cri

Yau Jumma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Japan Shinzo Abe, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar ta Sin.

Shugaba Xi ya yi maraba da zuwan Shinzo Abe kasar Sin, inda kuma ya yabawa niyyar da Abe ya nuna ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, wato ta kyautatawa, gami da kara raya dangantakar Sin da Japan. Xi ya nuna cewa, kasar Sin da kasar Japan makwabtan juna ne, kuma suna da babbar moriya kusan irin daya. Sin da Japan dukkansu kasashe ne masu karfin tattalin arziki, kana masu taka muhimmiyar rawa a duniya, don haka bunkasuwar dangantakarsu cikin dogon lokaci, kuma yadda ya kamata, na dacewa da moriyar jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangaren, Shinzo Abe ya ce, yana matukar farin-cikin samun damar kawo ziyara kasar Sin a daidai wannan muhimmin lokaci, wato lokacin cika shekaru arba'in da kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya, da sada zumunta tsakanin Sin da Japan. Ya ce yana fatan ta hanyar ziyarar sa a kasar Sin, kasashen biyu za su bude wani sabon babi ga ci gaban dangantakarsu dake kawowa juna alfanu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China