in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halartar Sudan ta kudu bikin baje kolin kasar Sin zai samar wa kasar tarin damammaki
2018-10-16 20:21:52 cri
Darakta mai kula da harkokin baje kolin hajojin cinikayya, a ma'aikatar cinikayya, masana'antu da harkokin da suka jibanci yankin gabashin Afirka na kasar Sudan ta kudu Christine Jino Okena, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, halartar Sudan ta kudu baje kolin hajojin da ake shigarwa kasar Sin, wanda aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba mai zuwa, zai samarwa kasar karin damammaki, na bunkasa fitar da hajojin ta zuwa kasashen ketare, tare da kara gano hanyoyin jawo jarin waje.

Christine Jino Okena, ya ce zuwan Sudan ta kudu baje kolin, zai taimakawa kasar wajen gano abokan hulda a fannin zuba jari, musamman a fannonin ayyukan gona, da raya al'adu, da hakar ma'adanai da dai sauran su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China