in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa Sin da Kenya za su daddale yarjejeniyar shigar da avocado kasar Sin
2018-10-19 16:26:26 cri
Jaridar Star ta kasar Kenya ta bayar da labari a ranar 17 ga wata cewa, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana yayin taron majalisar dokokin jihohin kasar da aka gudanar a kwanakin baya cewa, zai tashi zuwa birnin Shanghai na kasar Sin don halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, kana zai daddale yarjejeniyar shigar da avocado da mangwaro da kwallon cashew zuwa kasar Sin.

Shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, zai jagori tawagar wakilan manoma da 'yan kasuwa zuwa kasar Sin don halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko. Ya bayyana cewa, za a yi shawarwari kan cimma wasu yarjejeniyoyin ciniki a wurin bikin, wandanda za su bude kofar shigar da kayayyakin amfanin gona kashi 40 cikin dari na kasar Kenya zuwa kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China