Wata kiddiga ta baya-bayan nan da hukumar ta fitar, ta ce ya zuwa ranar Talata, akwai mutane 279 da aka yi wa rejistar cutar Ebola, da suka hada da wadanda aka tabbatar sun kamu da ita 244 da kuma wadanada ake kyautata zaton sun kamu guda 35, yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 179. Dukkan wadannan adadi an same su ne a lardin arewacin Kivu dake makotaka da lardin Ituri.
WHO ta yi gargadin cewa, bisa yanayin da ake ciki, har yanzu barazanar yaduwar cutar zuwa wasu lardunan kasar da kuma kasashe makwabta na da yawa.
Ta kara da cewa, yayin da take bibiyar yanayin barkewar cutar, nazarinta kan barazanar yaduwar cutar Ebola bai sauya ba, wanda ke nufi matakin a kasar da yankin na sama sosai, yayin da yake kasa a duniya.
Hukumar ta ci gaba da bada shawarar kada a haramta ziyarta ko cinikayya da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo saboda wadannan bayanai. (Fa'iza Mustapha)