RD-Congo: 'Yan adawa sun sanar da yin zanga zanga domin tilasta gudanar da zabuka bisa wa'adin kudin tsarin mulki
Wasu kungiyoyi mambobin kawancen 'yan adawa na jamhuriyar demokaradiyar Congo, musamman G7 da gamayyar kishin kasa, sun bayyana a ranar Jumma'a fara ayyukan zanga-zanga na gama gari a dukkan fadin kasar domin tilasta gudanar da zabuka bisa wa'adin kundin tsarin mulkin kasa. Hakan ya biyo bayan wata sanarwar siyasa da suka yi a birnin Kinshasa inda shugabannin adawar suka jaddada kin amincewarsu na ganin shugaba Joseph Kabila ya ci gaba da tsayawa kan mulkin bayan wa'adinsa dalilin rashin gudanar da zabuka a wannan shekara kamar yadda alkalan kotun kolin kasar suka bayyana. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku