in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar Cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta shiga wani muhimmin mataki, inda matakan takaita yaduwarta ke aiki
2018-09-01 16:13:11 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce barkewar Cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta shiga wani sabon mataki, inda ta ce yayin da matakan takaita yaduwar cutar ke aiki, ya kamata a kula da yanayin barkewar cutar.

Alkaluma na baya-bayan nan na nuni da cewa, ya zuwa ranar Larabar da ta gabata, an samu jimilar masu cutar 116 da suka hada da wadanda aka tabbatar 86, da wadanda ake kyautata zaton sun kamu 30, a cibiyoyin lafiya 5 dake arewacin lardin Kivu, da wani guda a lardin Ituri, yayin da kuma adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya kai 77, ciki har da 47 da aka tabbatar sun kamu da ita da wasu 30 da ake zaton sun kamu.

shekaru 35 ne matsakaicin shekarun wadanda ake zaton sun kamu, kuma kaso 56 cikinsu, mata ne.

An kuma samu jami'an lafiya 15 da ake tunanin sun kamu da cutar, inda aka tabbatar 14 daga cikinsu, yayin da guda ya mutu.

Hukumar WHO da abokan huldarta na aiki tare da jami'an kiwon lafiya da sauran al'ummomi domin wayar da kan jama'a game da matakan kariya da takaita yaduwar cutar, tare kuma da yi wa wadanda ke cikin barazanar kamuwa da ita rigakafi.

A cewar hukumar, matakan takaita yaduwar cutar na aiki. Kuma cikin makon da ya gabata, an samu raguwar masu mu'amala da wadanda suka kamu da cutar, kuma yawanci wadanda aka kwantar a cibiyoyin kula da masu cutar na samun kulawar da ta dace cikin sa'ar da aka tabbatar da suna dauke da ita, sannan an kara inganta aikin yi wa wadanda suka yi hulda da su riga kafi, domin kaiwa ga yawancin wadanda suka yi mu'amala da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar cikin makonni uku da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China