in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta tabbatar da barkewar cutar Ebola a yankin arewacin kasar
2017-05-13 12:47:40 cri
Ma'aikatar lafiya ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta tabbatar a jiya Jumma'a, da barkewar cutar Ebola a yankin arewacin kasar.

Ministan lafiya na kasar Oly Ilunga Kalenga ne ya sanar da Hukumar lafiya ta duniya WHO game da barkewar cutar Ebola a gundumar Bas-Uele dake arewacin kasar.

A cewar Ministan, an tabbatar da barkewar cutar ne bayan gudanar da gwaji kan samfurin jini a dakin gwaje-gwaje na cibiyar binciken kwayoyin hallita dake Kinshasa, babban birnin kasar.

Ministan ya kuma nemi taimakon hukumar lafiya ta duniya don karfafa yaki ta cutar.

A cewar Allarangar Yokouide, wakilin hukumar WHO a kasar, ya ce ofishin hukumar na aiki tare da hukumomin a matakin kasa da gundumomi tare da ofishin hukumar na yankin tsakiyar Afrika da hedkwatarsa da kuma sauran hukumomin wajen samar da kayayyakin aiki da jami'ai domin karfafa sa ido, da takaita yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China