Majiyar ta ce 'yan tawayen sun kuma kai hari kan sansanonin soji daban-daban dake Beni.
Wadanda suka tsira daga hare-haren, sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sai da 'yan tawayen suka saki wasu mutane daga cikin wadanda suka kama kafin daga bisani su kashe sauran.
Hukumomin soji sun bayyana cewa, har yanzu dai ana zaman fargaba a yankin
Gwamnatin Uganda ta dauki kungiyar ADF a matsayin ta ta'addanci. Tun asali, kungiyar ta kasance ne a yammacin Uganda kafin daga bisani ta fadada zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Congo dake makwabtaka da kasar. (Fa'iza Mustapha)