Rahotanni daga hukumar lafiya ta duniya WHO sun bayyana cewa, an fara gudanar da rigakafin ne a yankuna da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar. An kuma fara da yi wa ministan lardin, da jami'in tsare tsaren aikin rigakafin wannan allura, a aikin da ake fatan fadada shi, ta yadda dukkanin wadanda suka dace a yi musu allurar za su amfana. (Saminu Hassan)