in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci a dauki matakan magance matsalar tabin hankali dake shafar matasan Afrika
2018-10-11 10:15:52 cri
Wata babbar jami'ar hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana a wajen bikin tunawa da ranar masu fama da tabin hankali ta duniya cewa, kamata ya yi shugabannin gwamnatocin kasashen Afrika da abokan huldarsu na kasa da kasa su bada fifiko wajen lalibo bakin zaren magance karuwar matsalar tabin hankali dake addabar matasan nahiyar.

Matshidiso Moeti, daraktar hukumar WHO mai kula da shiyyar Afrika, ta lura cewa, ana samun karuwar matasa a nahiyar dake fuskantar matsalolin tabin hankali, don haka ta ce akwai bukatar daukar kwararan matakai domin dakile matsalar.

"A shiyyar Afrika, an yi kiyasa kashi 5 bisa 100 na matasa 'yan kasa da shekaru 15 suna fama da matsalar tabin hankali. Mafi yawa daga cikinsu ba'a cika lura da matsalar ko kuma a ba su magani ba, wanda idan al'amari ya yi nisa hakan yana iya zama babbar barazana ga lafiyar kwakwalwarsu," in ji Moeti.

Ta jaddada daukar kwararan matakai don tabbatar da dakile karuwar matsalar yawaitar masu fama da tabin hankalin a fadin nahiyar ta Afrika.

Kasashen Afrika sun bi sahun kasa da kasa wajen bikin tunawa da ranar masu fama da tabin hankali ta duniya wanda aka yi wa taken bikin na ba da "Matasa da kula da lafiyar kwakwalwa a yayin da duniya ke sauyawa". (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China