in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in diflomasiyar Sin ya yaba namijin kokarin ma'aikatan da ke aikin gina layin dogo na SGR a Kenya
2018-10-02 15:08:15 cri
Jami'in diflomasiya dake ofishin jakadancin Sin a kasar Kenya Li Xuhang ya yabawa ma'aikatan dake kula da layin dogo na SGR dake Kenya bisa namijin kokarinsu da ma yadda suke aiki a lokacin bikin cika shekaru 69 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, don tabbatar da cewa, komai na gudana kamar yadda aka tsara.

Li Xuhang ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin kasar Kenya cewa, bikin murnar kafuwar sabuwar kasar Sin da ake gudanarwa a ranar 1 ga watan Oktoban kowace shekaka, na daya daga cikin bukukuwa masu muhimmanci a kasar Sin.

Ya ce, zai yi amfani da wannan dama wajen yaba Sinawa dake wannan aiki saboda yadda suka sadaukar da kai duk da hutu mai muhimmancin da ake yi, kamar yadda ya bayyana a lokacin da ya ziyarci tashar layin dogon dake Nairobi.

Ya ce, an san Sinawa, da sadaukar da aiki ga aiki, wannan shi ne dalilin da ya sa na zo wannan tasha domin na gaida ma'aikatan, na kuma karfafa musu gwiwa.

Bankin shige da fice na kasar Sin ne dai ya biya kaso 90 cikin 100 na kudin aikin gina layin dogon mai tsawon kilomita 480 daga Nairobi zuwa Mombasan kasar Kenya, wanda kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin (CRGC) ya gina.

A shekarar 2017 ne kamfanin na CRBC ya kulla yarjejeniyar da kamfanin jiragen kasa na kasar Kenta (KRC) domin kula da layin dogon na SGR daga Mombasa zuwa Nairobi.

Li ya kara da cewa, yadda ma'aikatan suke aiki tukuru, zai taimaka wajen karfafa alakar dake tsakanin kasar Sin da Kenya, baya ga yadda hakan zai bunkasa jin dadin jama'a da tattalin arzikin kasar ta Kenya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China