in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na kokarin aiwatar da sauyin dake bisa wuyanta
2018-10-05 15:38:43 cri
Tarayyar Afrika AU, na tattaunawa da abokan huldarta na kasashen waje, don samun cikakken goyon bayansu ga shirye-shiryen samar da sauyi a kungiyar, bisa burinta na dogaro da kai.

A cewar mataimakin shugaban hukumar AU Kwesi Quartey, sauye-sauyen dake gudana a tarayya da aiwatar da matakan da aka dauka na samar da kudade, na da muhimmanci da kyakkyawan tasiri ga hadin giwa da abokan hulda, wanda ke nufin sauya dagantakarsu, daga mai karbar gudunmuwa zuwa abota ta kwarai.

A ranar Laraba da ta gabata ne mataimakin shugaban ya gudanar da wani taro da wasu abokan huldar tarayyar, domin tattaunawa da amincewa da jerin kwararan matakan dake da nufin samar da goyon bayan abokan huldar ga shirye-shiryen AU. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China