in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a saukaka tsadar sufurin jiragen sama a tsakanin kasashen Afrika
2018-10-03 15:33:41 cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU tana neman goyon bayan hanyoyin da za'a saukaka farashin sufurin jiragen sama a tsakanin kasashen Afrika.

Amani Abou Zeid, kwamishiniyar AU mai kula da sashen samar da kayayyakin more rayuwa, makamashi da yawon shakatawa, ta shedawa manema labarai a Nairobi cewa, kudaden da ake biya na sufurin jiragen sama a nahiyar Afrika yana da matukar tsada sakamakon rashin sassauta ka'idojin sashen sufurin a nahiyar.

Ta ce "Muna kokarin bullo da wani tsarin yawon shakatawa na nahiyar wanda zai bunkasa yadda za'a sassauta harkokin sufurin jiragen sama a Afrika. Daya daga cikin sakamakon da za'a samu ta hanyar tabbatar da 'yancin zirga zirgar jiragen sama a tsakanin kasashen Afrika shi ne zai kawo sauye sauye, za'a samu sufurin jiragen sama masu saukin farashi wadanda za su ci gaba da gudanar da ayyukan sufuri a Afrika domin tabbatar da bunkasa harkokin zirga zirga a cikin nahiyar." Zeid ta bayyana hakan ne a lokacin taron farko wanda karamin kwamitin harkokin yawon shakatawa dake karkashin kwamitin tsare tsaren sufuri, da zirga zirgar a tsakanin nahiyar da samar da kayayyakin more rayuwar, makamashi da yawon shakatawa nan a Afrika ya gudanar.

Zeid ta ce za'a sanya hannu kan tsara dabarun yawon shakatawa na nahiyar wanda shugabannin kasashen Afrika za su yi kana dukkan kasashen mambobin kungiyar AU za su mayar da tsarin na cikin gida a tsakiyar shekarar 2019.

Ta kara da cewa, yin takara a fannin sufurin jiragen sama zai taimaka wajen habaka fannin yawon bude ido a nahiyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China