in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwar Habasha sun yaba da kyakkaywar huldar cinikayyar dake tsakaninsu da kasar Sin
2018-10-31 10:44:42 cri
Masu ruwa da tsakani a harkokin zuba jari da kasuwanci na kasar Habasha a jiya Talata sun yaba da irin kyakkyawar mu'amalar cinikayya dake tsakanin kasashen Habasha da Sin, kana sun bukaci Sinawa masu zuba jari da su kara bada fifiko wajen zuba jarinsu a kasar ta Habasha.

Sun yi wannan tsokaci ne a lokacin a wani taron musayar ra'ayoyi tsakanin Habsha da Sin, wanda aka gudanar a ranar Talata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, da nufin bunkasa harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin bangarorin biyu.

Mataimakin kwamishina mai kula da hukumar zuba jari ta kasar Habasha, Anteneh Alemu, wanda ya jagoranci bude taron, ya tabbatar da cewa, kasar ta gabashin Afrika za ta ci gaba da janyo hankulan kamfanonin kasar Sin domin zuba jarinsu a kasarta.

Taron karawa musayar ra'ayoyin na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar kula da harkokin kasuwanci, masana'antu da zuba jari ta Habasha (ECCSA), da hukumar zuba jari ta kasar Habasha, da kuma majalisar kula da ciniki da shigi da ficin manyan injuna da kayan latironi ta kasar Sin.

Mataimakin babban sakataren kungiyar ECCSA, Wube Mengistu, ya bayyana cewa, kasar Habasha tana samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da kuma damammakin zuba jari a kasar, ya kara da cewa, a halin yanzu kasar Habashan tana matukar cin moriya daga bangaren fitar da kofi, da kayan amfanin gona da ake fitar da mai da kuma fatu zuwa kasar Sin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China