in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yaba da nadin mace a matsayin sabuwar shugabar Habasha
2018-10-26 09:36:02 cri

Tarayyar Afrika AU, ta yaba da nadin Sahle-Work Zewde a matsayin sabuwar shugabar kasar Habasha.

Sahle-Work Zewde, wadda ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kasa a tarihin Habasha, ta sha rantsuwar kama aiki ne jiya Alhamis, a gaban majalisun dokokin kasar biyu.

Wata sanarwar da shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat ya fitar, ta yi maraba da Sahle Zewde a matsayin shugabar kasar, tana mai cewa babbar nasara ce a fannoni da dama.

A baya, Sahle Zewde ta taba zama wakiliyar Habasa ta dindindin a Tarayya Afrika, haka kuma ta taba rike babban mukami a MDD.

A baya-bayan nan ne Habasha ta kafa sabuwar majalisar Ministoci, inda mata suka mamaye kaso 50 na mambobin majalisar.

Shugaban na AU, ya ce wannan ne karon farko a tarihin Habasha, da mace ta dare wannan babban mukami. Nadin dake zuwa bayan kafa majalisar da ya tabbatar da daidaiton jinsi, ya zama gagarumar ci-gaba ga karfafawa mata da ba su damar shiga cikin harkokin siyasa da na gwamnati. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China